Tunisiya

Tunisiya (Larabci:تونت، Abzinanci ⵜⵓⵏⴻⵙ; Faransanci: Tunisie). Jamhuriyar Tunisiya (Turanci Republic of Tunisia (Larabci : الجمهورية التونسية‎ al-Jumhūrīya at-Tūnisīya) kasa ce mai cin yancin gashin kanta a yankin arewacin Afrika, mai fadin kasa sukwaya mita 165,000 (sukwaya mil 64,000). Tayi iyaka da kasar Libya daga kudu maso gabas, sai Aljeriya daga yamma da kudu maso gabas, sai kuma da kogin miditaraniya daga Arewa da kuma gabas. Adadin kidayar mutanen Tunisiya a kidadayar shekara ta 2016 yakai miliyan 11.93. Sunan kasar Tunisiya ya samo asali ne daga sunan babban birnin kasar wato birnin Tunis.

colspan=2 | 
Tunisia - Location Map (2013) - TUN - UNOCHA
Tunisia - Location Map (2013) - TUN - UNOCHA

|- |

الجمهوريةالتونسية Jamāhīriyyah Tunisiya-
Flag of Tunisia Coat of arms of Tunisia
Location Tunisia AU Africa
Tunisia - Location Map (2013) - TUN - UNOCHA
Babban birni Tunis
Harshen kasa larabci
Manyan harsuna Larabcin Tunisiya, Faransanci, Abzinanci
Tsarin gwamnati Jamahuriya
Shugaban kasa Beji Caid Essebsi
Samun ƴancin kasa 20, Maris 1956
Fadin kasa 163.610 km²
Yawan mutane 11,304,482
Kabilu Larabawa 98%, Abzinawa 1%, Turkawa, Turawa, Yahudawa da sauran Kabilu kuma 1%.
wurin da mutane suke da zama 63/km2
kudin kasa Dinar (TND)
kudin da yake shiga kasa a shekara (74.97)$ miliyan
kudin da mutun daya yake samu a shekara (12,700)$
banbancin lokaci +1(UTC)
rane +1(UTC)
lambar yanar gizo .tn
Tuki Dama
Addini Musulunci 99.1% Sunnah,(.9 Shi'a, Baha'i, Maguzanci da Kiristanci)
lambar wayar taraho ta kasa da kasa +216

Tarihi

Daga tushe

Tarihi ya nuna cewar asalin kasar Tunisiya ta samo asaline daga Abzinawa wadanda suka kafu a hankali da kadan kadan a tsakankanin wadansu kananan kauyuka da kuma wadansu kananan mabanbantan kabilu. Mafi ya yawancin su sun gina kananan garuruwa domin gudanar da kasuwanci da fatake masu wucewa. A haka ne kauyukan abzinawan yaci gaba da karuwa sakamakon wadansu fataken na yada zango karshema sai suyi zaman su anan. Gabanin haihuwar Annabi Isah a tsakanin karnuka na 8 zuwa na goma birane suka kafu a kasar ta Tunisiya.

Kasasar Tunisiya ta fada hannun dauloli daban daban kamar daular Rumawa tsawon shekaru aru aru kafin samun yancinta.

Zuwan musulunci

A karni na Bakwai ne Larabawa suka ci kasar da yaki tare da gabatar Addinin Musulunci a kasar tare da gina wani birni wanda suke kira da Kairoun. Kairoun ne birni na larabawa musulmai na farko a kasar Tunisiya. Masarautun Musulunci da dama sun shugabanci Tunisiya. Daya daga cikin fitacciyar masarautar musulmai wadda ta jagoranci Tunisiya itace Masarautar Zirids. Zirids tana karkashin ikon masarautar Fatimiyya ce ta birnin Misra dake kasar Masar.

A haka kasar tunisiya taci gaba da zama karkashin daulolin musulunci har ya zuwa lokacin da turawan mulkin mallaka na kasar Faransa suka ahiga kasar a 12 ga watan Mayu, na 1881

Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe
Benin

Benin tana daya daga kasashin yamma Afrika kuma ita karamar kasa ce , da can ana cimata dukome , a shikara ta 1894 kasar faransa tamamaye tahar zuwa shikara ta 1960 tasamu incin kanta . Benin tanada iyaka da kasashi hudu sone:-

daga gabarcin Nijeriyadaga yammacin ta Togodaga arewacin ta Nijardaga arewa maso yammace burkina fasoBenin kasa ce me tsuw daga kuduance zuwa arewace (650 )km , kuma tsauwnta daga gabarce zuwa yammace ( 110 ) km , harshin faransanci shine yaren kasa tanada yawan mutane kemanin (4,418,000 ) a shikara ta 1988 baban birnen ta cotono yawan mutanen ta sunkai (1050) , Benin tanada yarurka masu dinbin yawa ( fun , adja buriya hausa dande ) da suran su

Burundi

Burundi ƙasa ne, da ke a nahiyar Afirka.

Gabon

Gabon (lafazi: /gabon/) ko Jamhuriyar Gabon (da Faransanci: République gabonaise), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Gabon tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 267,667. Gabon tana da yawan jama'a 1,979,786, bisa ga jimillar 2016. Gabon tana da iyaka da Kameru, da Gini Ikwatoriya kuma da Jamhuriyar Kwango. Babban birnin Gabon, Libreville ne.

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba (lafazi: /ali bonego onedimeba/) ne ; firaminista Emmanuel Issoze-Ngondet (lafazi: /emanuel isoze-negonede/) ne.

Gabon ta samu yancin kanta a shekara ta 1960, daga Faransa.

Gambiya

Gambiya (lafazi: /eritereha/) ko Jamhuriyar Gambiya (da Turanci: The Gambia ko Republic of the Gambia), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Gambiya tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 10,689. Gambiya tana da yawan jama'a 2,051,363, bisa ga ƙidayar jama'a a shekara ta 2017. Gambiya tana da iyaka da Senegal. Babban birnin Gambiya, Banjul ne.

Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow (lafazi: /adama baro/) ne. Maitamakin shugaban kasar Fatoumata Tambajang (lafazi: /fatumata tamebajaneg/) ce.

Gambiya ta samu yancin kanta a shekara ta 1965, daga Birtaniya.

Ghana

Ghana ko Gana ko Jamhuriyar Ghana(da Turanci: Republic of Ghana), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Ghana tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 238,540. Ghana tana da yawan jama'a 27,043,093, bisa ga jimillar 2014. Ghana tana da iyaka da Côte d'Ivoire, Togo kuma da Burkina Faso. Babban birnin Ghana, Accra ce. Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ne daga shekarar 2017. Mataimakin shugaban kasar Mahamudu Bawumia ne daga 2017.

Ghana ta samu yancin kanta a shekara ta 1957, daga kasar Birtaniya.

Gini

Gine ko Jamhuriyar Gine ko Gine-Conakry (da Faransanci: Guinée ko République de Guinée ko Guinée-Conakry), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Gine tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 245,857. Gine tana da yawan jama'a 13,246,049, bisa ga jimillar 2017. Gine tana da iyaka da Gine-Bissau, da Senegal, da Sierra Leone, da Liberiya, da Mali kuma da Côte d'Ivoire. Babban birnin Gine, Conakry ne. Shugaban kasar Gine Alpha Condé (lafazi: /Alfa Konde/) ne.

Gine ta samu yancin kanta a shekara ta 1958, daga Faransa.

Gini Ikwatoriya

Gini Ikwatoriya (lafazi: /gini iwwatoriya/) ko Ginen Ekweita ko Jamhuriyar Gini Ikwatoriya (da Ispaniyanci: República de Guinea Ecuatorial), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Gini Ikwatoriya tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 28,050. Gini Ikwatoriya tana da yawan jama'a 1,221,490, bisa ga jimillar 2016. Gini Ikwatoriya tana da iyaka da Kameru kuma da Gabon. Babban birnin Gini Ikwatoriya, Malabo ne.

Shugaban kasar Gini Ikwatoriya Teodoro Obiang Nguema Mbasogo (lafazi: /tehodoro obihaneg negema mebasogo/) ne ; firaminista Francisco Pascual Obama Asue (lafazi: /feransiseko fasekuhal obama asuhe/) ne.

Gini Ikwatoriya ta samu yancin kanta a shekara ta 1960, daga Ispaniya.

Komoros

Komoros kasar a Afirka ne.

Madagaskar

Madagaskar (lafazi: /madagasekar/) ko Jamhuriyar Madagaskar (da Faransanci: République de Madagascar; da Malagasy: Repoblikan'i Madagasikara), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Madagaskar tsibiri ne. Madagaskar tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 587,041. Madagaskar tana da yawan jama'a 24,894,551, bisa ga jimillar 2016. Babban birnin Madagaskar, Antananarivo ne.

Shugaban kasar Madagaskar Hery Rajaonarimampianina (lafazi: /heri rajonarimamepiyan/) ne daga shekarar 2014; firaminista Olivier Solonandrasana ne daga shekarar 2016.

Madagaskar ta samu yancin kanta a shekara ta 1960, daga Faransa.

Muritaniya

Kasar Muritaniya tana daya daga cikin kasashan Afrika ta yamma.

Namibiya

Namibiya A kasar a kudancin Afirka ne.

Nijeriya

Najeriya ko Nijeriya kasa ce dake nahiyar Afirka ta yamma. Tana da al'umman dasu kai fiye da mutum miliyan dari da saba'in da kabilun da suka haura 300. Hasali ma ita ce kasa ta uku a yawan kabilu a duniya. Najeriya ta samu mulkin kanta ne a 1 ga watan oktoba, shekarar 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Najeriya ta yi iyaka da kasashe uku; Daga arewacin kasar, akwai kasar Nijar , daga gabashi akwai Cadi da Kamaru, daga yammacin kasar akwai kasar Benin sannan daga kudancin kasar akwai tekun atalantik ko tabkin Gine.

A da, Lagos ne baban Birnin kasar kuma mazaunin gwamnati, amma a shekarar 1991 aka maida Abuja ta zama babban birnin Najeriya.

Saliyo

Saliyo ko Sierra Leone ƙasa ne dake Afirka, a yankin yammacin Afirka.

Senegal

Senegal ƙasa ne, da ke a yammacin Afirka.

Togo

Togo ko Jamhuriyar Togo (da Faransanci: République togolaise), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Togo tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 56,785. Togo tana da yawan jama'a 7,552,318, bisa ga jimillar 2015. Togo tana da iyaka da Liberiya, da Gine, da Mali, da Burkina Faso kuma da Ghana. Babban birnin Togo, Lomé ne.

Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbé ; firaminista Komi Sélom Klassou ne.

Togo ta samu yancin kanta a shekara ta 1960, daga Faransa.

Tunis

Tunis birni ne, da ke a ƙasar Tunisiya. Shi ne babban birnin ƙasar Tunisiya. Tunis ya na da yawan jama'a 2,643,695, bisa ga jimillar 2014. An gina birnin Tunis kafin karni na huɗu kafin haihuwar Annabi Issa.

Uganda

Uganda a kasar a Afirka.

Zambiya

Zambiya ko Jamhuriyar Zambiya (da Turanci: Republic of Zambia), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Zambiya tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 752,618. Zambiya tana da yawan jama'a 16,591,390, bisa ga jimillar 2016. Zambiya tana da iyaka da Tanzaniya, Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango, Angola, Zimbabwe, Malawi, Namibiya kuma da Mozambik. Babban birnin Zambiya, Lusaka ce. Shugaban kasar Zambiya Edgar Lungu ne daga shekarar 2015. Mataimakin shugaban kasar Inonge Wina ce daga 2015.

Zambiya ta samu yancin kanta a shekara ta 1964, daga Birtaniya.

Zimbabwe

Zimbabwe ko Jamhuriyar Zimbabwe (da Turanci: Republic of Zimbabwe), kasa ne, da ke a nahiyar Afirka. Zimbabwe tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 390,757. Zimbabwe tana da yawan jama'a 16,150,362, bisa ga jimillar 2016. Zimbabwe tana da iyaka da Afirka ta Kudu, da Botswana, da Zambiya kuma da Mozambique. Babban birnin Zimbabwe, Harare ne. Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa (lafazi: /emeresone menanegagewa/) ne daga shekarar 2017.

Zimbabwe ta samu yancin kanta a shekara ta 1965, daga Birtaniya.

A wasu harsuna

This page is based on a Wikipedia article written by authors (here).
Text is available under the CC BY-SA 3.0 license; additional terms may apply.
Images, videos and audio are available under their respective licenses.