Tarayyar Turai

Tarayyar Turai (EU) hukumar siyasa da tattalin arziki ne wanda ta kunshi ƙasashe arba'in da takwas da sun zama mamabobinta wanda ƙasashen na samuwa a nahiyar Turai. Tana da yawan fili kilomita 4,324,782; tana da kimanin yawan jamaá fiye da miliyen dari biyar da goma (510 million). Tarayyar Turai ta kafa kasuwa na ciki guda daidaitacciya ta amfani da tsarin dokoki da ke jagorantar 'Kasashen da ke mambobin wannan Tarayyar. Manufoffin Tarayyar ta nufa ýancin tafiye-tafiyen jamaá, kaya, aikace-aikace da kuma kudi tsakanin wannan Kasuwar ciki, da kuma kafa dokar adalci da harkokin gida da tsaren manufan kasuwancin, aikin noma, kasuwancin kifi da cingaban yankin. Tsakanin yankin Shengen, an kawas da ikon fasfo. An kafa hukumar kudi a shekara ta 1999 sai ta kafu da karfi a shekara ta 2002 da mambobin tarayyar Turai 19 wanda tana amfani da kudin Turai.

Tarayyar Tuarai na gudanar da hardaddiyar tsarin gwamnatocin ƙasashe wajen tsai da shawara. Manyan Hukumomi bakwai masu tsai da wadannan shawarwarin ana ce da ita Babban Kungiyar Tarayyar Turai, wanda ta kunshi; Majalisar Turai, Majalisar Tarayyar Turai, Majalisar Dokokin Turai, Hukumar Tarayyar Turai, Babban Kotun Tarayyar Turai, Babban Bankin Turai da kuma Fadar Oditocin Turai.

Tarayyar Turai ta samu asalinta daga kwalin Turai da alúmmar mulmula karfe (ESCS), da Hukumar Tattalin Arzikin Turai (EEC) wanda ƙasashe shida na cikin Tarayyar suka kafa a shekara ta 1951 da 1958. alúmmar da magadanta sun yi girma sabida damar shigar wasu ƙasashe da sun zama mambobi, ta kuma yi karfi wajen karuwar gyaran tsarin a wuraren da sun dace. Yarjejeniyar lokacin ta kafa Tarayyar Turai 1993 ta kuma gabatar da zaman dan Kasan Turai. Gyaran da aka yi na doka daga yau-yau na Tarayyar Turai, yarjejeniyar Lisbon ta kafu da karfi a shekara ta 2009.

Tarayyar Turai ta yawan jamaár duniya da kashi bakwai da digo uku na cikin dari (7.3%), Tarayyar ta sami kasafi da asa ta tanada (GDP) na tiriliyan 16.447 na dallar Amurka wanda ta tashi kashi 22.2 na cikin dari kusa kasafin da duniya ta tanada da kuma kashi sha shida da digo tara (16.9%) idan aka gwada da siyan iko daidaito. Ƙasashe 26 cikin 28 suna da matuka fihirisar mutanen raya ƙasa bisa ga ayyukan raya Ƙasar Majalisar Dinkin Duniya. A shekarar ta 2012, Tarayyar ta samu Lamba ta zaman lafiyar Nóbel. Ta hanyar tsarin tsaro da na ƙasashe, Tarayyar ta kuma tsumbure a hakkin harkokin waje da na tsaro. Tarayyar ta rike manzanci na ainihi a duniya baki daya kuma tana wakiltar kanta a Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Sanaá ta Duniya (WTO), G8 da G20. Domin gudumawarsu a duniya, Tarayyar tana da matukar iko na yau-yau.

EC-EU-enlargement animation
Taswirar Tarayyar Turai.

Jerin ƙasashen Tarayyar Turai

Aminu Waziri Tambuwal

AMINU WAZIRI TAMBUWAL

Aminu Waziri Tambuwal. An haife shi a ranar goma ga watan Junairu na shekara ta 1966, a garin Tambuwal da ke yankin kudancin jihar Sakkwato, wanda kuma ya fito daga zuri’ar Wazirin masarautar Tambuwal.

Bayan somawa da neman ilimin addini, sai ya soma neman ilimin zamani daga makarantar furamare ta Tambuwal, daga nan kuma sai ya zarce zuwa kwalejin horas da malamai ta gwamnati da ke Dogon-Daji inda ya kammala da samun takardar shaidar malanta mai daraja ta II a shekarar 1984. Daga nan sai ya samu gurbin karatun gaba da sakandare a jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, inda ya kammala da samun digirin farko a bangaren shari’a a shekarar 1991, haka kuma a bisa tanadin dokokin karatun shari’a, ya halarci makarantar horas da lauyoyi da ke Legas inda bayan karbar horo na shekara daya, sai aka tabbatar da shi a matsayin cikakken lauya a shekarar 1992.

Ko bancin karance-karance lamurran da suka shafi shari’a, honarabul Tambuwal ya halarci kwasa-kwasai iri-iri a kasashen ketare wadanda suka hada da na sanin ka’idojin sha’anin sadarwa wato ‘Telecoms Regulatory Master Class-Bath’ a Kasar Ingila a shekarar 2004, sai kuma kwas akan shata dokokin da suka jibanci bangaren sadarwa, wato ‘Lawmaking for the Communications Sectors’ a BMIT da ke Johannesburg ta kasar Afirka ta Kudu a shekarar 2004, har wa yau, ya halarci wani kwas akan yadda za a sanya ido akan tafiyar da kamfani a cikin tsari irin na gwagwarmayar neman kasuwa, wato ‘Regulating a Competitive Industry’ a Brussels ta kasar Beljiyam a shekarar 2005, a jami’ar Tulane kuwa, ya halarci kwas na tsara dokokin majalisa na kasa da kasa wato ‘International Legislative Drafting’ a shekarar 2005, ya halarci wani kwas akan cusa ra’ayi da daidaita matsaya wato ‘Influence and Negotiation’ a shahararriyar makarantar kasuwanci ta Stanford wato, ‘Stanford Graduate School of Business’ a shekarar 2008, da wasu kwasa-kwasai da dama.

A karon farko, an zabi honarabul Aminu Waziri Tambuwal a matsayin dan majalaisar wakilai mai wakiltar mazabar Kebbe da Tambuwal a majalisar wakilai ta kasa a shekarar 2003, a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta ANPP. Tun daga wannan lokacin tauraruwar farin jinin siyasarsa ta ci gaba da haskawa inda ya taba rike shugaban marasa rinjaye, ya kuma taba rike mukamin mataimakin babban mai tsawatarwa a zauren majalisar, mukamin da ya ci gaba da rikewa har zuwa karshen tafiyar majalisar wakilai zubi na shidda. Kuma ya taba zama jagoran ayarin ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya a nahiyar Afirka da Karebiyan da kuma gamin gambizar tawagar ‘yan majalisun kungiyar kasashen tarayyar Turai. Haka ma ya taba zama wakilin yanki na kungiyar ‘yan majalisun dokoki na kungiyar kasashe renon Ingila.

Honarabul Aminu Waziri, memba ne a majalisar zartaswa ta kungiyar lauyoyi ta kasa wato NBA, haka ma memba ne a kungiyar lauyoyi ta duniya, haka memba ne a kungiyar tsofaffin daliban makarantar koyon sha’anin gwamnati ta tsohon shugaban Amurka John F Kennedy, wato Kennedy School of Government’ da ke jami’ar Harvard ta kasar Amurka. Memba ne a kungiyar tsofaffin daliban makarantar koyon sha’anin kasuwanci ta Stanford wato Stanford Graduate School of Business’ da ke Amurka, memba ne a kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Tulane ta Amurka.

A gida Nijeriya, honarabul Tambuwal ya sami lambobim yabo da na karramawa iri-iri, kamar digirin girmamawa a fannin shari’a da jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato ta ba shi, domin yabawa da kawzonsa da kuma kokarinsa na ciyar da kasa gaba.

Aminu Waziri Tambuwal yayi takarar gwamnan jihar Sokoto a shekara 2015 karkashin jam'iyyar adawa ta APC, kuma yayi nasarar lashe zaben wanda ya bashi damar zama Gwamnan jihar ta Sokoto.

Andorra

Andorra, ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai. Andorra tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 468. Andorra tana da yawan jama'a 77,281, bisa ga jimilla a shekarar 2016. Andorra tana da iyaka da Faransa kuma da Hispania. Babban birnin Andorra, Andorra la Vella ne.

Andorra ta samu yancin kanta a shekara ta 1278.

Angela Merkel

Angela Dorothea Merkel (an haife ta a 17 ga watan Yulin 1954) yar'siyasar kasar Jamus ce wanda ayanzu itace Chancellor na Germany tun daga shekarar 2005. Tazama shugaban jam'iyyar Christian Democratic Union (CDU) daga 2000 zuwa 2018. Merkel an bayyana ta amatsayin de facto shugabar Kungiyar Tarayyar Turai, {{the most powerful woman in the world, da wasu masu sharhi amatsayin shugabar Free World.

Birtaniya

Birtaniya ko Biritaniya (da Turanci: Britain), kasa ne, da ke a nahiyar Turai. Biritaniya tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 242,495. Biritaniya tana da yawan jama'a 4,954,645, bisa ga jimillar 2016. Biritaniya tana da iyaka da Ayilan. Babban birnin Biritaniya, Landan ne.

Magana sosai, Birtaniya, ta ƙunshi Ingila, Weyilz kuma da Sukotilan. United Kingdom (da Hausanci: Masarautar Ɗaya ko Masarautar Haɗaɗɗe), ya ƙunshi Ingila, Weyilz, Sukotilan kuma da Ayilan ta Arewa. Tsibirin Birtaniya, ya ƙunshi Ingila, Weyilz, Sukotilan, Ayiland ta Arewa, kuma da kasar Ayilan.

Sarauniyar Birtaniya Elizabeth ta Biyu (lafazi: /elizabet ta biyu/) ce. Firaministan Birtaniya Theresa May (lafazi: /teresa mai/) ce. Margaret Thatcher dai itace macen farko data zama Firaministan ƙasar Birtaniya.

Birtaniya ta samu yancin kafin karni na goma.

Wikimedia Commons on Birtaniya

Eiffel Tower

Eiffel Tower (furucci|aɪfəl; furucci da faransanci|tuʁ‿ɛfɛl|) wani wrought-iron lattice tower dake a Champ de Mars a birnin Faris, ƙasar Faransa. An mata suna ne da sunan injiniyan da kamfaninsa suka tsata da gina ta, shine Gustave Eiffel.

An gina ta daga 1887 zuwa 1889 amatsayin itace mashigi zuwa 1889 World's Fair, da fari tasha suka daga wasu daga cikin manyan masu zanen ƙasar faransa da malamai akan taswirar ta, sai dai tazama cultural icon na duk duniya baki daya ga Faransa da kuma gina mafi shahara a duniya. Eiffel Tower itace gurin da akafi ziyarta da kudi a duniya; mutane miliyan 6.91 suka hau karshen ta a shekarar 2015.

Tana da tsawon kimanin 324|m|ft|0, kamar tsayin gini mai hawa 81, kuma itace gini mafi tsawo a Faris. Kasan shi square ne, wanda keda fadin |125|m|ft|0 a kowane sashe. Lokacin gininsa, Eiffel Tower ya zarce Washington Monument yazama mafi tsayin gini da dan'adam ya gina a duniya, haka ta rike na tsawon shekaru 41 harsai da Ginin Chrysler na Birnin New York ta kammalu a 1930. Saboda sanya aerial na kafofin yada labarai a saman ginin a shekarar 1957, ayanzu tafi Ginin Chrysler da tsayi 17|ft|m. Amma banda transmitters. Eiffel Tower itace ta biyu gini mafi tsayi da basu da kariya a Faransa bayan ginin Millau Viaduct.

Ginin na matakai uku ga masu ziyara, da gun cin abinci a matakin farko da na biyu. Matakin farko na sama 276|m dake sama da ƙasa – itace mafi tsawon observation deck wanda kowa ka iya amfani dashi a Tarayyar Turai. Ana sayar da tikiti dan hawa saman da matakalu ko lift zuwa kaiwa matakin farko data biyu. Kaiwa sama daga matakin ƙasa zuwa matakin farko yafi matakala 300, haka ma daga hawa ta farko zuwa ta biyu. Dukda akwai gurin takawa zuwa sama, amma kawai anfi samun yin amfani da lifta (na'ura) ne.

Faransa

Faransa (faransanci:République française) tana daya daga Kasashen Turai tanada iyaka da kasar beljik da kasar suwysra da luksanburk kuma dakwai wane kowgi da yarabata da Birtaniya tanada shahararan dan wasan kallon kafa ana cemasa Zinedine Yazid Zidane.

Faransa, bisa ga hukuma jamhuriyar Farasanci Kasa ne ta musamman da hadin kai tare da cibiyoyin yammancin Turai da kuma wasu yankunan Kasashen waje da cibiyoyin. Sashen Turai na Faransa wanda ake kira alkaryar Faransa ta mike har Bahar maliya zuwa hannun Tekun Turai da Tekun arewa da kuma daga mahadin zuwa Tekun phasa. Danin Faransa 643,801 murabba’in kilomita kuma tana da yawan jama’a miliyan 67.6. kuma tana da hardaddiyar shugabanci a jamhuriyarta wanda birnin tarayyarta na a Farista, wanda ita ce babban birni na al’adu da ta cibiyar kasuwanci. Tasrin mulkin Faransa ta nuna Kasar ta boko ce da ta dimokaradiyya wanda sarautarsa na samowa daga jama’ar.

A zamanin dá, wanda yanzu alkaryar Faransa ne dá tana da mutanen Gaul, kananan mutane. Daular Romawa sun ci mutanen Gaul da yaki a shekara ta 51 BC kafin zuwan Kiristi, wanda ta rike Gaul zuwa shekaru 486. Mutanen Gaul ta Roma sun fuskanci hare-hare da kaurace-kaurace daga ýan Faransa ta Jamus wanda sun mamaye yankin shekaru aru-aru, daga baya suna kafa Daular Faransa na dá. Faransa ta fito muhimi wajen mulki na Turai a shekaru na karshe ta tsakiya, da nasararta cikin shekaru dari na yaki (1337 zuwa 1453) wanda ta karfafa ginin Kasar Faransa da ba da dama na gaba a mulukiya innanaha na tsakiya. A cikin lokacin farfadowa, Faransa ta fuskanci cin gaban al’adu makake da farkon kafuwar Daular mulkin mallaka na zamani. Yakin basasa na addini tsakanin ýan Katolika da ýan Furotesta, ta mamaye karni na goma sha shida (16th).

Faransa ta mamaye Turai wajen a’adu, da siyasa da mulkin soja kalkashin Louis. Masu ilimin falfasa sun taka rawa mai kyau a lokacin wayewan kai a karni na goma sha takwas (18th), an hambarar da mulukiya a juyin mulkin Faransa. A cikin gadonta da bayanin hakkin ‘dan Adam da na ‘dan Kasa, daya daga cikin takardu na hakkin ‘dan Adam, wanda tana bayyana cewa Kasar ta dace har wa yau. Faransa ta zama daya daga cikin tarihin zamani a jamhuriya na farko sai da Napoliya ya hawo mulki sai ya kafa Daula ta farko na Faransa a shekara alif dari takwas da hudu (1804). Ya dingi fada da rikitattun gwiwa cikin lokacin yake-yaken Napoliya, ya mamaye harkokin Turai fiye da shekaru goma wanda ya shafa al’adun Turai na tsawon lokaci. Faransa ta jimre hayaniyar gadon gwamnatoci a faduwar Daular, mulukiyar ta gyaru. An mayar da shi a shekara ta alif dari takwas da talatin(1830) bisa dokan mulukiya, sannan a gurguje a jamhuriya ta biyu, kuma a Daula ta biyu har zuwa kafuwar jamhuriyar farasanci na uku mai karfi a shekara ta 1870. Jamhuriyar farasanci sun yi rikice-rikice da Ikilisiyar Katolika don rashin wa`azin addinin kirista a faransa a lokacin juyin mulkin farasanci a kafuwar dokar Laicité na shekara 1905. Laicité ya yi tsamani amma haryar cimma buri ne na boko wanda shi ne muhimmin dokan gudanarwa a zamanin yau na hukumar faransanci.

Faransa ta kai tsawo na yankinta cikin karni na sha tara (19) da farkon karni na ashirin (20), zuwa karshe, ta mallaki babban Daula ta biyu na mulkin mallaka a duniya. A yakin Duniya na farko, Faransa ta zo daya daga cikin masu nasara a cikin ninka sau uku tsakanin Kasashe kawance fadan yaki da mulkin tsakiya. Faransa dá kuma daya ne cikiin masu iko a Yakin Duniya na biyu, amma ta zo a kalkashin mamayar kusuwar mulki a shekara ta 1940. Bin kwaton ýanci a shekara ta 1944, Jamhuriya ta hudu ta kafu sai aka narkar da ita a sanadiyar Yakin Aljeriya. An kafa Jamhuriya ta biyar a shekara ta 1958 wanda Charles de Gaulle ya shugabance ta, kuma tana nan har wa yau. Yawancin Daulolin farasanci an bar yin musu mulkin mallaka a Yakin Duniya na biyu.

A cikin tarihinta duka, Faransa ta zama na gaba a duniya da cibiyar al’ada, tana yin muhimmin gudumawa kan Kimiya da Fasaha da Ilimin Falfasa. Faransa ta halarce gaggarumar lamba na uku a kungiyar Kyautata Ilimi da Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya na Turai a wajajen gadon duniya (bayan Italya da Sfen) kuma tana karban Ýan Yawon Shakatawa kusan miliyan tamanin takwas (83) a shekara fiye da kowane Kasa a duniya. Faransa ta kasance da iko na al’ada muhimi na tattalin arziki, na soja da na siyasa. Ita Kasa ce mai cigaban masana’antu da zama lamba na shida a tattalin arziki a duniya babba ta bin kasafin da Kasa ta tanada, kuma ta zo na tara babba wajen Sayayyan wuta daidaito. Bisa ga Credit Suisse, Faransa ita ce na hudu mafi arziki a Kasashen duniya bisa ga jimilar arzikin gidaje. Ta kuma mallake babban bangare mafi tattalin arziki a duniya (EEZ), wanda Kasarta ta ci murabba’in Kilomita 11,691,000 (4,514,000 sq mi).

‘Yan Farasanci suna jin dadin daidaitacciyar zama, kuma Kasar tana da martaba sosai wajen ilimin Kasashe, kiwon lafiya da ababan rayuwa `yanci da doka ta tanada da kuma raya dan Adam. Faransa tana daga kasashen da sun kafa majalisar Dinkin Duniya wanda ta zama daya daga cikin mambobi biyar na ainihi na ‘yan tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya. Ita kuma mamba ta kungiya ta bakwai (7), Kungiyar Yarjejeniya na Phasa ta Arewa (NATO), Kungiyar Hadin Kai don Rayar da tattalin Arziki (OECD), Kungiyar Sana’a ta Duniya (WTO) da kuma La Francophonie. Faransa ta samar da Tarayyar Turai Kuma na gaba a cikin Tarayyar.

Liechtenstein

Liechtenstein ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai.

Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya dai tsari ne wanda kasashen duniya suka amince da kerawa domin magance rikice rikice da yake yake bayan yakin duniya na Biyu (2). An kafa ta ne a 1945 domin sayya kwaciyar hakkali a cikin duniya baki daya. Kuma ta kumshi kusan dukannin kasashen duniya, banda kasashe biyu; palestinu da Saint-siege.Muhimmin Jawabin da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana game da Hakkokin Yan-adam a shekarar 1948.

Moldufiniya

Moldufiniya ko Maldoba ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai. Babban birnin Moldufiniya, Chisinau ne.

Monaco

Monaco (lafazi: /monako/) ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai. Monaco ya na da iyaka da ƙasashen Faransa da Italiya.

Moroko

Maroko ko Moroko Larabci المغرب , (Al-Magrib) (ma'ana mafadar rana ko yamma). A yaren Abzinawa kuma ⵍⵎⵖⵔⵉⴱ Faransanci Moroc, cikaken sunan kasar shine Masarautar Maroko da yaren Abzinanci ko kuma Berber ⵜⴰⴳⵍⴷⵉⵜ ⵏ ⵍⵎⵖⵔⵉⴱ da Larabci kuma المملكة المغربية‎ Al-mamlaka al-magrabiyya Kasace dake bin tsarin mulki salon sarauta dake Arewacin Afrika. Kasace ta asalin yan kabilar Abzinawa. Kasr Maroko kasace dake da dogayen tsaunuka da kuma Sahara.

Al'umar kasar Maroko yakai kimanin miliyan 33.8 kuma tana da adadin fadin kasar da yakai kilomita 446,550 (sukwaya mil 172 410). Babban birnin taraiya shine Rabat, kuma birni mafi girma shine Kasablanka. Sauran birane masu girma sun hada da Marrakeah, Tangier,Sale, Fea da kuma Meknes.

Yaren Berber ko Abzinanci shine babban yare kuma mai asali a kasar kafin Larabci da ya shigo bayan mamayar da larabawa sukayi ma kasar. Musulunci ne babban addini na kasar.

Palestin autonomija

Zirin Gaza kamar yadda sunansa ya nuna, wani ɗan zirin yanki ne da ke gaɓar tekun mediteranian, wanda yake a ƙarƙashin mulkin ‘yan Hamas. Garin ya yi iyaka da ƙasar Misra daga kudu maso yamma da kuma ƙasar Isra'ila ta ɓangaren Arewa da gabas. Gaba ɗaya tsawon garin bai wuce mil 25 ba, faɗinsa kuwa bai wuce mil 4-8 ba. Hukumar Falasɗinawa iƙrarin mallakar wanannan ziri a matsayin wani ɓangare na Falasɗinu.

An kafa yankin zirin gaza ne a shekarar 1948, lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta raba ƙasar Falasɗinu gida biyu ta baiwa Yahudawa rabi. To mutanen da suke a ɓangaren da aka baiwa Isra'ila sune aka kwashe su aka kai su yankin da yanzu ake kira gaza a matsayin ‘yan gudun hijira. To tun daga wannan lokaci ne fa yankin zirin gaza ya tsinci kansa a wani hali na tsaka mai wuya. Kasancewar ƙasar Isra'ila wadda ta mulki wannan guri tun daga shekarun 1967-2005, ita ce har yanzu take da ikon tafiyar da harkokin sararin samaniyar zirin gaza da iyakar garin daga ɓangaren ruwa, da harkokin sufurin ruwa da kuma iyakar dake tsakanin isra'ila ɗin da Gaza.

Wannan iko da Isra'ila take da shi, wanda kuma Hamas take adawa da shi, shi ne ya baiwa Isra'ila damar nuna isa akan dukkan abubuwan shige-da fice a wannan yanki na Gaza, wanda ya haɗa da abinci. A duk lokacin da abinci ya yi ƙaranci to fa al'ummar zirin gaza ba su da wata dama illa ta dogaro da samun abinci ta hanyar Cibiyoyin agajin abinci na duniya dake aiki a wannan yanki.

Tun lokacin da aka kafa zirin na Gaza sai ya kasance ƙarƙashin kulawar ƙasar Misra, tun daga 1948-1967, kafin yaƙin 1967 wanda aka yi tsakanin Isra'ira da Larabawa inda Isra'ila ta mamaye zirin gaza. kuma a yau ita misirance take da ikon tafiyar da harkokin kan iyakarta da zirin gaza.

Yankin na zirin gaza dai ya samo sunan sa ne da garin gaza, wanda shi ne babban birni a wannan yanki. Zirin Gaza na da yawan al'umma da suka kai kimanin miliyan ɗaya da rabi.

Hukumar Falasdinawa ta samu ikon karɓar harkokin mulki a shekara ta 1994 a ƙarƙashin yarjejeniyar birnin Osolo, wadda ta sa Isra'ila ta janye daga mulkin Zirin Gaza a 1994. To sai dai wannan yarjejeniya ta Osolo ta baiwa Isra'ila ikon ci-gaba da mallakar harkokin sararin samaniyar gaza da ruwayen yankin da kuma harkokin ruwan, da harkokin rijistar ƙidaya da shige da ficen baƙi da shigar da kayayyaki da kuma fitar da su, sannan da harkokin kuɗin shiga.

A shekara ta 2006 aka gudanar da zaɓe a Falasɗinu inda Hamas ta lashe wannan zaɓe da babban rinjaye, ta kayar da jam'iyyar Fatah da sauran tsirarun jam'iyyu, wanda hakan ya baiwa Isma'il Haniya damar zama zaɓaɓɓen Firaministan Falasɗinu. To sai dai Isra'ila da Amirka ba su amince da wannan zaɓe da Falasɗinawa suka yiba, kasancewar su a wajensu Hamas ƙungiya ce ta ‘yan tarzoma. Wanda sakamakon haka yasa ƙasar Isra'ila da Amirka da Kanada da Tarayyar Turai suka dakatar da dukkan kuɗaɗen hukumar Falasɗinu. Inda rashin daidaituwar gwamnati da rashin kuɗi da kuma yunwa da ƙishirwa ta sa dole wasu daga cikin al'ummar Falasɗinu su kai hijira.

Rikici ya ɓalle tsakanin Hamas da Fatah saboda halin da aka shiga na kiki-kaka, wanda hakan ya sa sai da ƙasar Saudiyya ta shiga tsakani, inda ta samar da yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu tare da kafa gwamnatin haɗin-gwiwa. Wannan yarjejeniya ce ta sa Isma'il Haniya ya yi murabus daga matsayinsa na zaɓaɓɓen firaministan Falasɗinu a dimokuraɗiyyance, zuwa firaministan riƙon ƙwarya na gwamnatin haɗingwiwa. An kuma rantsar da shi a matsayin shugaban sabuwar gwamnati a ranar 18, ga Maris, 2007.

A ranan 14 ga Juni, 2007 shugaban Falsɗinawa Mahmoud Abbas ya kori Isma'il Haniya ya naɗa Salam Fayyad a matsayin Firaministan gwamnatin haɗin gwiwa, canjin da majalisar dokokin Falasɗinawa ta ce bata yarda da shi ba domin ya saɓa doka. Shugaban ƙasa na da ikon sauke firaminista amma ba shi da ikon naɗa wani sai da izinin majalisa. Wannan dalili ne ya sa Haniya ya koma Gaza ya ci-gaba da zama mai mulkin zirin-gaza.

Tun daga lokacin da Hamas ta karɓe mulkin Gaza kawo yau, wannan yanki na gaza yake cikin talala. Dukkan hanyoyin shiga gaza guda 5 da sukai iyaka da Isra'ila, Isra'ilan ta toshe su. Sai dai kawai idan taimakon gaggawa ko na agaji ya taso. Halin da ya sa al'ummar Falasɗinawa cikin halin ƙaƙanikayi.

Isra'ila dai tana iƙirarin cewa duk tana yin wannan ne, saboda Hamas ta ƙi yarda ta amince da ita a matsayin halattacciyar ƙasa, kuma Hamas ɗin tana harba rokoki a cikin ƙasar Isra'ilan. Isra'ilan ta ce matuƙar Hamas ta yarda da halaccin kafuwarta ta kuma daina harba mata rokoki, to za ta buɗe iyakokin Gaza ta kuma daina kai hare-haren da take kaiwa Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Ita kuma Hamas tana iƙirarin cewa ba za ta amince da Isara'ila a matsayin Halattacciyar ƙasa ba, ba kuma za ta daina harba rokoki cikinta ba, har sai ta sakarwa Falasɗinawa mara, kuma sai ta janye daga inda ta mamaye zuwa inda yarjejeniyar 4 ga Yuni, 1967 ta amincewa Isra'ila, sannan kuma ta sakar musu harkokin shige-da fice da tattalin arziki ta kuma basu dama su gina filayen jiragen sama da na ruwa dadai sauransu. Su rayu cikin aminci kamar sauran al'ummar duniya.

Sallar mata na kasa da kasa a Turkiyya

A wannan mako zamu tattauna batutuwa game da ranar sallar mata da aka gudanar na kasa da kasa rana ta takwas watan Maris.

Wanna sallar kasa da kasa ne ke gudanarwa inda aka yi Allah wadai masu cin mutuncin mata.Rana ce wanda ake gudanarwa don a yi shella ga barin wulakanta mata kuma a tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata. An sake lura da rayuwar mata da aikin tattalin arziki ciki har da cinikayya da suke yi.A wanna shirinmu zamu tattuana yadda lamarin kasuwanci ke tafiya dangane da mata, wato yadda za a bambanta su.

An nemi shuagabannin kasashe su dinga ba mata karfi gurin tattalin arziki, su nemi shawo kanmatsaloli da mata ke fuskanta don samun kansu gurin karfafa tattalin arziki da kuma yadda za a taimaka musu gurin dabarun gyara tattalin arziki, duk da haka gudunmuwar da mata ke sakawa cikin tattalin arziki ba shi da yawa.Wanna matsala ne sosai da ya kamata a tattauna, don haka dole mu kuma m duba ainihin yadda za a magance batun nan gaba.

Sau da yawa mata ba sa samun hanyar neman ilimi yadda ya kamat sabili da haka ne samun aikin su keda wuya.Aikin gida da aikin sana’a da suke yi ko da yaushe ya yi sanadiyar rashin yin aiki mtaukar aiki a kowane bangarori da suke.Saboda haka ma ba sa iya amincewa da kansu gurin aiki ba..Ayyuka Kaso biyu daga uku da kudi kaso daya daga goma da kuma dukiya daya daga dari ne mata zasu kwashi.

Musamman a kasashe masu tasowa maza na sama da mata a cikin kowanne fanni. A kasashe masu matukar ci gaba kuma ba za a ce akwai daidaito tsakanin mata da maza ba. A kasashen Amirka da nahiyar Turai ana gwagwarmaya don daidaito tsakanin mata da maza guin karban albashi da samun matsayin shuagabancin guraren aiki da kuma yadda gwamnati za ta taimakawa mata masu renon yara.

A Amirka abubuwa da dama sun toshe hanyar aikin mata.matsalar basu iznin idan sun haifu wato babu dokoki na kasa wanda ya ba mata damar zama gida yadda ya kamata don su rene yararsu.kowanne kafani da nashi doka, tun bin da ya shafi mata masu yara, da iyalai da kuma kai yara makarantu ko gidan rikon yara jarirai daga safe zuwa yamma duk na da tsada sosai.Dole sai matada kansu su zauna gida don su rene yaran.Bincike da aka yi a kasar Jamus kuma ta nuna cewa mata kaso saba’in da uku sun ce babu wani ragawa da aka yi wa mata masu renon yara. Wani maudu’i dangane da mata ne albashi da ake bambantawa tsakanain maza da mata.A bincike da aka fitar gurin ijara ko kuma albashi a Amirka, wato aiki da namiji zai yi ya karbi albashi dala daya idan mace ta yi za a biya ta Sent tamanin da biyu abu wnada bai kai dala daya ba.

Kasar Jamus na daga cikin kasa wanda mata ke fuskantar bambanci gurin aikin yi.

Sanarwa da aka fitar sakamakon bincike da tarayyar ma’aikata IG suka fitar sun gano cewa mata kaso sittin da takwas sun samu hayaniya gurin rashin adalci da aka nuna musu gurin biyan albashi.Hakazalika kaso sittin da takwas din kuma sun ce har ila yau ba a basu damar shuagabancin guraren aiki ba.

Sanarwa da kungiyar kula da aiki na kasa da kasa ta yi ta nuna cewa nan zuwa shekaru saba’in za a dinga samun rashin daidaito gurin aiki tsakanain mata da maza.

Kungiyar ta ce aiki kaso saba’in da bakwai da maza da mata ke yi maza ne ke samun albashi sama da mata duk da nuna himmar aiki da mata ke yi.Ta ce wannan daidaito babu wata kasa da ta daidaita batun.Bincike kuma ta nuna cewa ba samu mata da rashin aiki ko rashn zuwa aiki ba shekrau ishirin da suka gabata amma duk da haka ba samu daidaito gurin biyan albashi ba,dole ta kimanta cewa ba za a samu shawo kanmtalolin ba nan da shekaru saba’in.Binciken kuma ta nuna cewa batu din ta yadu sosai a kasashen musulmai da kuma kasashen gabas ta tsakiya.

A kasar Turkyya matsaloli da wulakanci da mata ke fusknata sun kunshe rashin samun damar karatu, rashin samun damar aikin kaow musu jalli,mummunan al’adu,da bambanci gurin aiki.Bincike da Tarayyar Turai ta yi dangane da haka ta nuna cewa samun damar aiki wato mata sun kwashi kaso hamsin da bakwai bisa dari a nahiyar Turai sai a Turkiyya mata sun kwashi kaso ishirin da shida bisa dari. Sai idan an zo gurin samun damar karatu kuma mata a nahiyar Turai sun kwashi kaso hamsin da takwas sai a Turkiyya mata sun kwashi kaso arba’in da uku bisa dari.

Duk da haka, da aka yi bincike game da kungiyoyi da ayyukan gwamnati an samu cewa kasar Turkiyya ta zo na biyu a duniya kasa wato wanda mata kaso goma sha daya ke nana a matsayin shuagabanannin kafanoni.A shekara ta dubu biyu da goma sha hudu ne kungiyar kula da aiki na kasa da kasa suka wallafa wata litattafi game da aikin mata da bambancin jinsi.A cikin wanna littafi har ila yau a cikin kasashe dari da takwas kasashe tamanin ne suka ba mata shuagabanci gurin aiki a kamfanoni.

Ga littafin, kamfanonin ayyukan gwamnati ne ta samu ma mata guri amma a kamfanonin kasuwanci dai rashin shuagabancin mata batu ne da ya kamata a duba sosai nan gaba.A kasashe goma sha tara babu wani kamfani da ya dauki mace a matsayin shugaba wato a kasar Norway mata a matsayin shuagaban ma’aikata kaso goma sha uku ne wato kaso mafi yawa a duniya sai Turkiyya ta biyo na biyu da kaso goma sha daya.

Da aka bincika mata a matsayin shugaban ayyukan gwamnati a duniya , kasar Jmaika ne ta samu kaso hamsin da tara sai kasar Yaman ta samu kaso biyu wato kasa wanda ba ta ba mata samun damar shuagbancin ma’aikata ba.A cikin wannan jerin kasashen duniya wanda suka nada mata a matsayin shaugabannin gwamnati, Amirka ta zo na goma sha biyar,Rasha ishirin da biyar,Ingilan arba’in da daya sai Turkiyya tasa’in da hudu.

Gwmantin Turkiyya ta kafa ma’aikatar gwamnati mai kualwa da harkokin mata don nuna himmar da kasar keda gurin kula da hakin dan dama. Ana sa ran kasar Turkiyya za ta samu cigaba sosai game da hakan nan gaba.

TRT HAUSA

San Marino

San Marino ko Jamhuriyar San Marino, ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai. San Marino tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 61,2. San Marino tana da yawan jama'a 33,285, bisa ga jimilla a shekarar 2016. Andorra tana da iyaka da Italiya. Babban birnin San Marino, San Marino ne.

San Marino ta samu yancin kanta a shekara ta 301.

Tattalin arzikin duniya

Abu ne sanannne kuma a hukumance cewa, rikicin tattalin arzikin Amirka ya zama ruwan dare gama duniya. To amma duk da haka wasu ƙasashen sun fi wasu taɓuwa idan ana batun matsayin irin illar da rikicin yai wa ƙasashen duniya. Wato ma'ana idan Amirka abin ya shafeta 100 bisa 100, to su ƙasashen da rikicin yai wa sauƙin taɓawa, abin bai wuce da kashi 1 zuwa 20 bisa dari ya shafe su ba.

Ƙasa ta farko da ba ta jin wannan rikici na tattalin arzki a jikinta, ita ce Tarayyar Daular Larabawa, wato "United Arab Emirates:". Duk da cewa tana da matsalar cikin gida na batun hallata kuɗin haram, amma dai duk da haka arzikin ƙasar yana ci gaba da haɓaka, kamar ma ba su san da wani rikicin tattalin arzikin duniya ba.

Ƙasar ta biyu ita ce ƙasar Armeniya. Itama duk da cewa tana da rikicinta na cikin gida ta ɓangaren rashin yin cuɗanya da kasuwannin duniya, don haka tana buƙatar bunƙasa shirinta na kasuwanci tsakanin ƙasa da ƙasa. To sai dai kuma labari mai daɗin shi ne, rashin yin wani ƙasaitaccen kasuwanci na ƙasa da ƙasa ya kare ta daga faɗawa dumu-dumu cikin rikicin tattalin arzikin da duniya ta tsinci kanta. Kai wasu ma na ganin cewa, ita ya kamata ta zamo ta farko a cikin ƙasashen da wannan rikicin na tattali bai shafa ba?

Ƙasa ta uku da rikicin tattalin arziki bai shafa sosai ba ita ce Maroko. Ko dadai ita Maroko ta yi dumu-dumu wajen harkokin cinikayya tsakanin ƙasa da ƙasa, musamman ma dai da ƙasar Faransa, da kuma batun harkokin yawon buɗe ido, waɗanda ake ganin waɗannan hanyoyi guda biyu suna samun tawaya saboda rikicin tattalin arzkin da Amirka ta jazawa duniya. To sai dai kuma labari mai daɗin shi ne, ma'adanan ƙarƙashin ƙasa da Allah ya huwace wa ƙasar, sun isa su ba ta ikon maye gurbin duk wani abu da za ta iya rasawa sakamkon rikicin tattalin arzikin.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Dogwayen gine-ginen birnin Kuala Lumpur a MalesiyaKasa ta huɗu a duniya wajen rashin jin raɗaɗin rikicin tattalin arziki ita ce ƙasar Malesiya. Duk da cewa Malesiya ta kai iya wuya wajen yin hulɗar cinikayya da Amirka, to amma abin daɗin shi ne, kamfanonin Amirkan da suke buƙatar rage yawan kuɗaɗen da suke kashewa, yanzu haka ƙasar Malesiyan suke komawa suna sarrafa kayayyakinsu a can, saboda sauƙin biyan ma'aikata.

Ƙasa ta biyar kuwa ita ce Iran. kuma ya ɗan shafe ta ne saboda hulɗar kasuwancin da take yi da ƙasashen Turai, duk da cewa tana yin hakan ne a ƙarkashin takunkumi. To amma labari mai daɗi ga Iran shi ne cewa, ba ta yin hulɗar kasuwanci da Amirka, ƙasar da ta haddasa rikincin tattalin arzikin. Sannan tana daga cikin ƙasashen da suke sayar da mai ga ƙasar chaina, wanda ake ganin ko wannan ciniki na mai da chaina kaɗai ya isa ya riƙe ƙasar Iran tsawon shekaru goma.

Ƙasa ta shida it ace ƙasar Koriya ta Arewa: Labari mara daɗi a gare ta shi ne, babu baki masu sanya jari a cikin harkokin noma da bunƙasa samuwar abinci a wannan kasa, to amma kuma ware tan da aka yi ba a hulɗar ciniki da ita sosai, ya sanya matsalar tattalin arziki ta sa me daidai ruwa daidai tsaki.

Ƙasa ta bakwai kuwa ita ce, ƙasar Tailan. Kuma abin ma da ya sa rikicin ya shafe ta shi ne, kasancewar babban kamfanin da ke gudanar da harkokinsa a ƙasar wani reshe ne na kamfanin inshorar nan na Amirka AIG, wanda rikicin tattlin arzikin Amirka ya fara rutsawa da shi. To amma labari mai daɗin shi ne, ƙasar ta dogara ne da mfani da tsaɓar kuɗi da kuma ciniki na ƙeƙe-da ƙeƙe wajen harkokin kasuwanci.

Daga ƙasar Tailan sai Romaniya. rikicin ya ɗan shafi Romaniya ne, saboda yadda ta ɗan yi zurfi wajen cinikayya da tarayyar Turai da kuma yadda take ciniki kai tsaye da sauran ƙasashen waje. To sai dai abin farin ciki ga ƙasar shi ne, har yanzu tana nan a matsayin ƙasar da kamfanonin nahiyar Turai suka ɗauka a matsayin wani sansani na hada-hadarsu.

To ƙasa ta tara ita ce ƙasar Brazil. Kuma rashin sa'ar da tai shi ne cewar, ƙasar Amirka ita ce babbar abokiyar cinikinta. To amma kuma labari mai daɗi ga ƙasar shi ne na kasancewarta a wani matsayi na samun yarjejeniyar kasuwanci na ƙasa da ƙasa tsakanin ta da ƙasar Indiya da Chaina. Wanda waɗannan ƙasashe biyu yanzu haka suna matsayi na ƙoli-ƙoli a haɓakar tattalin arziki a duniya.

Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Takardar kuɗin Chaina ta Yuan 100Ƙasa ta goma kuwa a jerin ƙasashen da raɗaɗin rikicin tattalin arziki ya taɓa da sauƙi-sauƙi ita ce ƙasar Chaina. Kuma illar da wannan rikici yai mata shi ne, na yadda ƙasar Amirka da ƙasashen nahiyar Turai sukai tsananin rage buƙatar kayayyaki daga gare ta. Kuma har yanzu hakan na ci gaba da yin tasiri akan tattalin arzikinta. To amma kasancewar Chaina a matsayin ƙasa mafi yawan al'umma a duniya, hakan ya sa tattalin arzikin yana jure rikicin, saboda dogaro da take da shi akan kayayyakin da al'ummar ƙasar ke buƙata da kuma sauran ƙasashen da rikicin bai taba su sosai ba, irin su Brazil. Sannan kuma har ila yau Chaina na dogaro da irin tsabar kuɗin da take bin amirka bashi, musamman ma dai ta fuskar rancen da take bayarwa domin ceto masana'antun Amirkan da ga rugujewa.

Vatican

Vatican ko Vatikan, ƙasa ne, da ke a nahiyar Turai. Vatican tana da yawan fili kimani na kilomita murabba'i 0,44. Vatican tana da yawan jama'a 1,000, bisa ga jimillar a shekarar 2017. Vatican tana da iyaka da Italiya.

Ita ce fadar Fafaroma, har ila yau Birnin ne cibiyan mabiya kiristoci na darikar katolika suke zaune.

Zirin Gaza

Zirin Gaza kamar yadda sunansa ya nuna, wani ɗan zirin yanki ne da ke gaɓar tekun mediteranian, wanda yake a ƙarƙashin mulkin ‘yan Hamas. Garin ya yi iyaka da ƙasar Misra daga kudu maso yamma da kuma ƙasar Isra'ila ta ɓangaren Arewa da gabas. Gaba ɗaya tsawon garin bai wuce mil 25 ba, faɗinsa kuwa bai wuce mil 4-8 ba. Hukumar Falasɗinawa iƙrarin mallakar wanannan ziri a matsayin wani ɓangare na Falasdinu.

An kafa yankin zirin gaza ne a shekarar 1948, lokacin da Majalisar dinkin Duniya ta raba ƙasar Falasdinu gida biyu ta baiwa Yahudawa rabi. To mutanen da suke a ɓangaren da aka baiwa Isra'ila sune aka kwashe su aka kai su yankin da yanzu ake kira gaza a matsayin ‘yan gudun hijira. To tun daga wannan lokaci ne fa yankin zirin gaza ya tsinci kansa a wani hali na tsaka mai wuya. Kasancewar ƙasar Isra'ila wadda ta mulki wannan guri tun daga shekarun 1967-2005, ita ce har yanzu take da ikon tafiyar da harkokin sararin samaniyar zirin gaza da iyakar garin daga ɓangaren ruwa, da harkokin sufurin ruwa da kuma iyakar dake tsakanin isra'ila ɗin da Gaza.

Wannan iko da Isra'ila take da shi, wanda kuma Hamas take adawa da shi, shi ne ya baiwa Isra'ila damar nuna isa akan dukkan abubuwan shige-da fice a wannan yanki na Gaza, wanda ya haɗa da abinci. A duk lokacin da abinci ya yi ƙaranci to fa al'ummar zirin gaza ba su da wata dama illa ta dogaro da samun abinci ta hanyar Cibiyoyin agajin abinci na duniya dake aiki a wannan yanki.

Tun lokacin da aka kafa zirin na Gaza sai ya kasance ƙarƙashin kulawar ƙasar Misra, tun daga 1948-1967, kafin yaƙin 1967 wanda aka yi tsakanin Isra'ira da Larabawa inda Isra'ila ta mamaye zirin gaza. kuma a yau ita misirance take da ikon tafiyar da harkokin kan iyakarta da zirin gaza.

Yankin na zirin gaza dai ya samo sunan sa ne da garin gaza, wanda shi ne babban birni a wannan yanki. Zirin Gaza na da yawan al'umma da suka kai kimanin miliyan ɗaya da rabi.

Hukumar Falasdinawa ta samu ikon karɓar harkokin mulki a shekara ta 1994 a ƙarƙashin yarjejeniyar birnin Osolo, wadda ta sa Isra'ila ta janye daga mulkin Zirin Gaza a 1994. To sai dai wannan yarjejeniya ta Osolo ta baiwa Isra'ila ikon ci-gaba da mallakar harkokin sararin samaniyar gaza da ruwayen yankin da kuma harkokin ruwan, da harkokin rijistar ƙidaya da shige da ficen baƙi da shigar da kayayyaki da kuma fitar da su, sannan da harkokin kuɗin shiga.

A shekara ta 2006 aka gudanar da zaɓe a Falasdinu inda Hamas ta lashe wannan zaɓe da babban rinjaye, ta kayar da jam'iyyar Fatah da sauran tsirarun jam'iyyu, wanda hakan ya baiwa Isma'il Haniya damar zama zaɓaɓɓen Firaministan Falasdinu. To sai dai Isra'ila da Amirka ba su amince da wannan zaɓe da Falasɗinawa suka yiba, kasancewar su a wajensu Hamas ƙungiya ce ta ‘yan tarzoma. Wanda sakamakon haka yasa ƙasar Isra'ila da Amirka da Kanada da Tarayyar Turai suka dakatar da dukkan kuɗaɗen hukumar Falasɗinu. Inda rashin daidaituwar gwamnati da rashin kuɗi da kuma yunwa da ƙishirwa ta sa dole wasu daga cikin al'ummar Falasɗinu su kai hijira.

Rikici ya ɓalle tsakanin Hamas da Fatah saboda halin da aka shiga na kiki-kaka, wanda hakan ya sa sai da ƙasar Saudiyya ta shiga tsakani, inda ta samar da yarjejeniyar zaman lafiya a tsakaninsu tare da kafa gwamnatin haɗin-gwiwa. Wannan yarjejeniya ce ta sa Isma'il Haniya ya yi murabus daga matsayinsa na zaɓaɓɓen firaministan Falasdinu a dimokuraɗiyyance, zuwa firaministan riƙon ƙwarya na gwamnatin haɗingwiwa. An kuma rantsar da shi a matsayin shugaban sabuwar gwamnati a ranar 18, ga Maris, 2007.

A ranan 14 ga Juni, 2007 shugaban Falsɗinawa Mahmoud Abbas ya kori Isma'il Haniya ya naɗa Salam Fayyad a matsayin Firaministan gwamnatin haɗin gwiwa, canjin da majalisar dokokin Falasɗinawa ta ce bata yarda da shi ba domin ya saɓa doka. Shugaban ƙasa na da ikon sauke firaminista amma ba shi da ikon naɗa wani sai da izinin majalisa. Wannan dalili ne ya sa Haniya ya koma Gaza ya ci-gaba da zama mai mulkin zirin-gaza.

Tun daga lokacin da Hamas ta karɓe mulkin Gaza kawo yau, wannan yanki na gaza yake cikin talala. Dukkan hanyoyin shiga gaza guda 5 da sukai iyaka da Isra'ila, Isra'ilan ta toshe su. Sai dai kawai idan taimakon gaggawa ko na agaji ya taso. Halin da ya sa al'ummar Falasɗinawa cikin halin ƙaƙanikayi.

Isra'ila dai tana iƙirarin cewa duk tana yin wannan ne, saboda Hamas ta ƙi yarda ta amince da ita a matsayin halattacciyar ƙasa, kuma Hamas ɗin tana harba rokoki a cikin ƙasar Isra'ilan. Isra'ilan ta ce matuƙar Hamas ta yarda da halaccin kafuwarta ta kuma daina harba mata rokoki, to za ta buɗe iyakokin Gaza ta kuma daina kai hare-haren da take kaiwa Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Ita kuma Hamas tana iƙirarin cewa ba za ta amince da Isara'ila a matsayin Halattacciyar ƙasa ba, ba kuma za ta daina harba rokoki cikinta ba, har sai ta sakarwa Falasɗinawa mara, kuma sai ta janye daga inda ta mamaye zuwa inda yarjejeniyar 4 ga Yuni, 1967 ta amincewa Isra'ila, sannan kuma ta sakar musu harkokin shige-da fice da tattalin arziki ta kuma basu dama su gina filayen jiragen sama da na ruwa dadai sauransu. Su rayu cikin aminci kamar sauran al'ummar duniya.

Κατηγορία:Παλαιστίνη

A wasu harsuna

This page is based on a Wikipedia article written by authors (here).
Text is available under the CC BY-SA 3.0 license; additional terms may apply.
Images, videos and audio are available under their respective licenses.