Duniya

Duniya halitta ce daga cikin dimbin duniyoyin dake cikin sararin samaniya. Hakika wannan duniya da muke ciki yar karama ce idan aka kwatanta ta da sauran duniyoyi kamar duniyar Jupiter. duniyar da muke ciki itace ta uku tsakaninta da Rana daga cikin abinda ake kira wato falakin duniyoyi da turanci kuma solar system. Kuma ita kadai ce a yanzu dai aka samu halitta mai rai a cikinta. Ita kadaice koramu da Teku ke gudu a doronta amma sauran duniyoyin ko Iska babu a cikinsu, ballantana har akai ga samun abu mai rai.

Hakika Allah shine mahaliccin komai shi kadai ne yasan abinda ya dace da Bayinsa shi yasa ya zabar mana wannan duniya domin ita kadaice za a iya rayuwa aciki.

Solar system
wannan sune duniyoyin dake cikin sararin subuhana wato Solar system

Zuwan dan adam sararin samaniya; abu mai yiwuwa da mara yiwuwa [1]

Fannin ilimin Sararin Samaniya (Astronomy) na daga cikin abubuwan da suka fi kayatar da ni, da wasu dimbin jama’a da nake da yakinin hakan su ma yana kayatar da su. Sai dai ba zai yiwu lokaci daya a gama fasaltawa mutum irin dimbin abubuwan mamaki da Allah Ta’ala Ya taskance a cikin sararin samaniya ba. Don haka, na hakaito mana wani dogon jawabi da wani shahararren masanin sararin samaniya mai suna Edward Tellar ya yi, mai cike da abubuwa muhimmai a shekarar 1961, dangane da tafiya zuwa sararin samaniya. A cikin jawabinsa ya fadi abin da yake ganin zai iya yiwuwa, da abin da yake ganin ba zai yiwu ba.Da farko ya yi hasashen cewa daga shekarar da ya yi bayanin a wancan lokaci,wato 1961, ba za a kai shekara ta dubu biyu (2000) ba har sai an samu damar zuwa duniyoyi da ke makwabtaka da duniyarmu ta Earth kamar su Mars, da benus da Jupiter da kuma duniyar wata. Sai dai a cewarsa, `”Mene ne burin da muke son cin mawa idan mun ziyarci wadannan duniyoyi? Shin, za mu koma duniyoyin ne mu ci gaba da rayuwa ko kuwa ‘ya’yanmu ne za su mai da rayuwarsu zuwa can?’’Ya ci gaba da cewa “Za a iya tunanin zuwa can domin samo abubuwa masu daraja kamar su zinare, da azurfa da yuraniyon, sai dai kuma zinare da azurfa ana kokarin lalubo su a nan duniyarmu, shi kuwa sinadarin yuraniyon, dauko shi daga wata duniyar zuwa wannan duniyar tamu abu ne mai matukar hadari. Kawai dai abin daza mu so mu dauko shi ne abu mara nauyi,wanda mu a nan muka rasa shi; wannan ba komai ba ne sai Ilimi.’’Edward ya ci gaba da cewa, “Kasancewar Rana daya ce daga cikin Taurari kimanin guda biliyan dari dake cikin rukunin taurarin gungun taurari (Galady) wanda aka baiwa suna “Milky Way,” ba lalle ne a ce duk cikin taurarin nan Tauraruwarmu (Rana) ita kadai ce ke da duniyoyin da ba wanda zai iya rayuwa a cikin su. Haka kuma ba gungun taurarinmu (Galady) ne kadai ba; akwai wani gungun taurari (Galady) dake makwabtaka da mu mai suna “Andromeda Galady),” wanda aka yi hasashen nisansa da gungun taurarinmu ya kai nisan da idan ka tura haske zai yi shekaru miliyan biyu kafin ya isa wajen (2 million light years). Bayan gungun taurarin “Andromeda”, akwai wasu miliyoyi irinsa. Daga can gefe, daura da wannan gungun taurari iya nisan zangon tafiyar haske shekaru miliyan dari, akwai wasu gungun taurari (Galady) guda biyu dasuka yi karo da juna, wanda hakan ya samar da wani kara mai tsanani tare da fitar wani rada (Radar), wanda a cewarsa sai da ya keto har cikin sararin samaniyar duniyarmu.A cikin bincikensa, Edward Teller ya tabbatar da cewa a duniyar Mars akwai wasu launuka masu wulkitawa a duk saddaaka kalli duniyar ta amfani da madubin hangen nesa mai suna “Spectroscope”. Mutum zai ga wasu alamomi da suke nuna alamun wanzuwar wasu hade-haden sinadarai da suke tabbatar da cewa akwai rayuwa a duk inda aka same su, wato sinadaran “Carbon-Hydrogen Bond,” irin sinadaran da ake samu a cikin man fetur. Malaman kimiyyar man fetur kuma sun tabbatar da cewa abin da ke samar da man fetur shi ne rubewar matattun abubuwa kamar su halittun ruwa da sauransu. Don haka, ta yiwu samun wadancan sinadarai a wurin na da nasaba da samun rayuwar halittu a can, sai dai zai yi wahala a samu mutane kamar mu masu rayuwa a can duk da dai muna da burin zuwa can kuma za mu je.

Mars Earth Comparison 2
Dubi bambancin duniyarmu da duniyar Mars

Wani abin kuma shi ne, a kimiyar ilimin sinadarai (Chemistry) mun sani cewa dukkan wani abu mai rayuwa a nan duniyatushensa daya ne, domin muna da tabbacin irin kwayoyin halittar dake jikin mutum; akwai wasu a jikin biri, da kifi, cututtuka masu rai da dai sauransu. Abin tambayar a nan shi ne; shin, idan akwai halittu masu rayuwa a duniyar Mars tun d ga sinadaran da aka gano a can kuma da akwai irinsu a jikin mutum dama sauran halittun dake nan duniya, shin, tsatsonmu daya da su kenan ko kuwa kowa tsatsonsa daban? Ina da tabbacin dai ba mu kadai neke rayuwa ba a cikin sararin wannan duniya. Amma kuma wani abu mai rikitarwa shi ne; a hasashen da aka yi, wannan duniya tamu ta yi shekaru biliyan goma da wanzuwa. Rayuwar mutane kuma a duniyarmu ta wanzu kimanin shekaru rabin miliyan zuwa milkiyan, ai kuwa za a samu masu rai da suka rayu tun farkon duniyoyin nan kafin wanzuwarmu, lalle zan so na ji ina wadanncan mutane dasuka rayu gabaninmu suka tafi?Sai ya ce zuwanmu duniyar wata ne zai ba da damar hango nisan zangon da a nan duniyar ba za mu iya hangowa ba, har daga bisani a tabbatar da cewa duniyar gungun taurari ba ta da iyaka, ko kuma watakila a hango iyakarta da ma wasu biliyoyin irinta. Da akwai wani abu mai launin ja da ya taba bayyana a duniyar Jupiter tun a karnin da ya wuce, wanda zuwa yanzu ba a san ko mene ne ba kuma ana ganin shi kadan-kadan har zuwa yau. Don haka, zuwanmu daya daga cikin duniyoyi masu makwabtaka da mu ne zai sa mu samu ilimin sauran duniyoyin da mana wasu abubuwan.Sai dai a cewarsa, duk wadannan ba su ne manyan muhimman abubuwan ba. A matsayinmu na mutane masu numfashi, babban abin da muka fi so mu sani shi ne amsar tambayar nan da wasunmu suka sha yi: shin, akwai abu mai rai a duniyar wata da sauran duniyoyi? Domin ni ban yarda da fadar mutane cewa halittun da kerayuwa a sauran duniyoyi (Martians) wai kamu daya ba ne, kuma kalarsu koriya ce. Bayan haka kuma za mu so mu ji shin, a cikin Sararin samaniya akwai duniyoyi masu dauke da mutane irinmu? Daga nan sai mu kara bincike akan kara nkanmu. Haka kuma, mu nce muna so kafin karshenkarnin nan mu zagaye duniyoyin Rana (planets), shin, yaushe za mu fara tafiya zuwa sauran taurari? Tauraruwa dai mafi kusanci da Tauraruwarmu rana itace PROdIMA CENTAURI, ba kamar yadda wasu ke cewa “Alpha centauri” ba, kuma nisan dake tsakanin Tauraruwa, rana da “Tauraruwa Prodima,” nisan tafiyar haske ne a shekaru hudu, (4 light years). Ga shi kuma kamar yadda masanin nan Einstein ya fada, babu wani mahaluki da zai iya yin gudu a wani abin hawa dai-dai da saurin haske matukar yana da nauyi, sai dai idan zai zamo ba shi da nauyi ko kadan.To amma duk da haka, ko da za mu iya tafiya dai-dai da gudun haske, tazarar shekaru hudu ba karamar tafiya ba ce, ga shi kuma lalle muna so sai mun je “Prodima Centauri.” Sannan alal misali, idan yanzu na yi amfani da kayayyaki na wannan zamani, na’urar Rocket din da zan iya kerawa zai yi gudu dai-dai daya bisa ashirin na gudu da saurin haske (1/20), kenan idan muka durfafi “Prodima,” ba za mu iya kaiwa gare ta ba sai nan da shekaru tamanin! Wannan lokaci ne mai tsawon gaske.

Space Shuttle Columbia launching
Wannan kumbo kenan a tashar yan sama jannati na Columbia kafin a cillashi zuwa sararin samaniya

Flanetis dake sararin Samaniya

  • Mercury
  • Venus
  • Earth
  • Mars
  • Uranus
  • Saturn
  • Jupiter
  • Neptune
  • Pluto

Duniyar Jupiter

Jupiter wata irin duniya ce mai ban al'ajabi saboda tasha banban da sauran duniyoyi gaba daya.

The Earth seen from Apollo 17
inner planet
bangare naEarth-Moon system Gyara
farawa4540 million years BCE Gyara
name in kanaちきゅう Gyara
named afterƘasa (shinfidar ƙasa) Gyara
wuriInner Solar System Gyara
located on terrain featurecircumstellar habitable zone Gyara
coordinates of easternmost pointno value Gyara
coordinates of northernmost point90°0′0″N 0°0′0″E Gyara
coordinates of southernmost point90°0′0″S 0°0′0″E Gyara
coordinates of westernmost pointno value Gyara
highest pointMount Everest, Chimborazo Gyara
lowest pointChallenger Deep Gyara
creatorno value, Big Bang Gyara
catalog code806.4616.0110 Gyara
studied byEarth sciences, geology, geophysics Gyara
parent astronomical bodyRana Gyara
type of orbitorbit of Earth, heliocentric orbit Gyara
dissolved, abolished or demolishedunknown value Gyara
tutaflag of the Earth Gyara
has qualityEarth mass, Earth's magnetic field, planetary habitability Gyara
manifestation ofopen system Gyara
notationEarth symbol Gyara
opposite ofsky Gyara
shapegeoid Gyara
geography of topiclabarin ƙasa Gyara
tarihin maudu'ihistory of the world, history of Earth Gyara
Dewey Decimal Classification550, 910.02, 525 Gyara
Wolfram Language entity codeEntity["Planet", "Earth"] Gyara
WordLift URLhttp://data.thenextweb.com/tnw/entity/earth Gyara

Anazarci

  1. http://www.dailytrust.com.ng/aminiya/index.php/kimiya-da-fasaha/7510-zuwa-sararin-samaniya-abu-mai-yiwuwa-da-mara-yiwuwa-1 "zuwa sararin samaniya abu mai yiwuwa da mara yiwuwa"
Afirka

Nahiyar Afirka itace nahiya ta biyu a fadin kasa da kuma yawan jama'a a duniya. Nahiyar da ke daya daga cikin nahiyoyi bakwai na duniya tanada kasashe kimanin hamsin da hudu kuma akwai ruwayoyi da dama da ke nuna yadda nahiyar Afirka ta samo asalin sunanta na Afirka ɗin, to amma dai ruwaya mafi shahara da kuma karɓuwa a tarihi itace, wadda ke cewar, sunan Afirka ya samo asali ne daga kalmar Misirawa ta "Afru-ika" wadda ke nufin "Ƙasar Haihuwa". Idan mutum ya kira kansa ɗan Afirka ko Ba'afirke, hakan na nuni da yadda mutum yake danganta sunansa da nahiyar Afirka a matsayin mahaifarsa. Kamar dai yadda bisa al'ada, idan mutum ya fito daga Amurika, sai a kira shi Ba'amurke, ko kuma idan daga Turai mutum ya fito sai a kira shi Bature. Hakama wanda ya fito daga ƙasashen Larabawa sai a kira shi Balarabe da dai sauransu.

Zauren taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ke birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, abun da ya kamata masu karatu su fahimta shi ne, duk da an ce sunan Afirka ya samo asali ne daga harshen mutanen Misra, to ba ana nufin harshen Larabci tsantsa ba. Domin dukkanin ƙasashen da ke magana da harshen Larabci kowannen su yana da irin nasa karin harshen, amma tsantsar Larabci na nahawu wanda aka fi sani da 'FUSHA', Larabci ne da harshen alƙur'ani ya zo da shi.

Babu shakka haka batun yake, kuma dalilin da ya sa ma sunan Afirka ɗin ya samu daga harshen Misiranci shi ne, kasancewar shi harshen Misirancin da dadadden harshene kuma yana da tasiri sosai akan harsuna na asali kamar su harshen Girka da na Latin, kodadai dukkaninsu ana kiran su da suna harsuna 'yan asalin indiya da Turai, wato 'Indo-European languages', a Turance kenan. Kuma ita kanta kalmar ta 'Indo' ta samu ne daga kalmar Indiya, kuma ita kalmar Indiya ta samu ne daga wajen Larabawa lokacin da suka mamaye yankin na Indiya ɗin. Bayan da suka gano cewa Wani mutum da ake kira Kush ɗan Ham, yana da 'ya'ya biyu masu suna "Hind," da "Sind." To shi Hind ɗan Kush sai ya kafa daula a Indiya, shi kuma 'Sind' ɗan Kush sai ya kafa daula a yankin Larabawa. To daga nan ne Larabawa suke kiran al'ummar Indiya da suna 'Hindu'.

Tarihi dai ya nunar da cewa, tasirin da harshen Misarawa yake da shi a duniyar Larabawa da ma wasu yankuna na Afirka ya samu ne sabo da yawan fina- finai da wasannin kwaikwayo da kuma waƙe-waƙen mutanen misra da suka cika yankin. Sannan kuma kamar yadda Misirawa suke kiran mutanen da suka fito daga yankin Afirka da "Afru-ika" Su kuma mutanen Latin suna kiran afirkawan ne da nasu harshen inda suke cewa da su "Africanus" Wadda ke nufin daga Afirka". To amma kuma an fara amfani da kalmar Afru-ika lokaci maitsawo kafin a fara amfani da ta Africanus. Domin kuwa tun shekaru 400 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis-salam, har zuwa shekaru 400 bayan komawar sa ga Allah, Rumawa sun kasance ne a arewacin Afirka. Su kuwa Girkawa sun kasance ne a Misira daga wajejen shekaru 300 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihissalam, zuwa kimanin shekaru 200 bayan komawarsa ga Allah.

Asiya

Wikimedia Commons on Asiya

Falasdinu

Falasdinu (Turanci Palestine), (Larabci فلسطين ) دولةفلسطين Daular Falastin kasa ce da ake tababa a kanta a nahiyar Asiya. Kasar na ikirarin mallakar yankin gabar tekun yammacin ta wato (iyaka da kasar Isra'ila da Jordan) sai kuma yankiin Gaza (iyaka da Israila da Masar) da kuma gabashin birnin Jerusalem wanda shine kasar take dauka a matsayin babban birnin ta, dukda yake kuma a birnin Ramallah ne ale tafiyar da mafi yawan aiyukan gwamnati. Mafi yawancin yankunan kasar Falasdinu na karkashin Yahudawan Israila yan kama guri zauna da suka kwace tun daga ahekarar 1967. Yawan mutanen kasar ya kai 4,560,368 kidayar 2014, itace kasa ta 123 a yawan jama'a a duniya.

Bayan kammala yakin duniya na biyu a 1947, Majalisar dinkin duniya tayi kokarin kafa kasar ta Falasdinu wadda ta kumshi Larabawa Musulmai, da kuma Yahudawa da kasar su ta Israila a 1948. Bayan kafa kasar ta Falasdinu ne sai larabawa Musulmai suka dauki makamai domin nuna adawa da yin hakan tare da yakar yahudawa.

Tun daha nan yakin yaita ci gaba tare da canza salo kala kala har zuwa ranar 15 Nuwamba 1988, ina shugaban Falsdinawa Yaseer Arafat, ya ayyana kafa kasar ta Falasdinu a birnin [[Aljas][ na kasar Aljeriya. Shekara daya kuma bayan sa hannun kan yarjejeniyar Osla Accords a 1993 gwamnati ta kafu a kasar Falsdinu.

Kasashe 136 mambobi a majalisar dinkin duniya ne suka amince da Falasdinu a matsayin kasa. Kasar har yanzu ba mamba bace ba a Majalisar dinkin duniya, amma kuma mamba ce a kungiyar kasashen larabawa wato G77, da kuma Hukumar wasanni ta Olympic da sauran manyan kungiyoyin duniya.

Faransa

Faransa (faransanci:République française) tana daya daga Kasashen Turai tanada iyaka da kasar beljik da kasar suwysra da luksanburk kuma dakwai wane kowgi da yarabata da Birtaniya tanada shahararan dan wasan kallon kafa ana cemasa Zinedine Yazid Zidane.

Faransa, bisa ga hukuma jamhuriyar Farasanci Kasa ne ta musamman da hadin kai tare da cibiyoyin yammancin Turai da kuma wasu yankunan Kasashen waje da cibiyoyin. Sashen Turai na Faransa wanda ake kira alkaryar Faransa ta mike har Bahar maliya zuwa hannun Tekun Turai da Tekun arewa da kuma daga mahadin zuwa Tekun phasa. Danin Faransa 643,801 murabba’in kilomita kuma tana da yawan jama’a miliyan 67.6. kuma tana da hardaddiyar shugabanci a jamhuriyarta wanda birnin tarayyarta na a Farista, wanda ita ce babban birni na al’adu da ta cibiyar kasuwanci. Tasrin mulkin Faransa ta nuna Kasar ta boko ce da ta dimokaradiyya wanda sarautarsa na samowa daga jama’ar.

A zamanin dá, wanda yanzu alkaryar Faransa ne dá tana da mutanen Gaul, kananan mutane. Daular Romawa sun ci mutanen Gaul da yaki a shekara ta 51 BC kafin zuwan Kiristi, wanda ta rike Gaul zuwa shekaru 486. Mutanen Gaul ta Roma sun fuskanci hare-hare da kaurace-kaurace daga ýan Faransa ta Jamus wanda sun mamaye yankin shekaru aru-aru, daga baya suna kafa Daular Faransa na dá. Faransa ta fito muhimi wajen mulki na Turai a shekaru na karshe ta tsakiya, da nasararta cikin shekaru dari na yaki (1337 zuwa 1453) wanda ta karfafa ginin Kasar Faransa da ba da dama na gaba a mulukiya innanaha na tsakiya. A cikin lokacin farfadowa, Faransa ta fuskanci cin gaban al’adu makake da farkon kafuwar Daular mulkin mallaka na zamani. Yakin basasa na addini tsakanin ýan Katolika da ýan Furotesta, ta mamaye karni na goma sha shida (16th).

Faransa ta mamaye Turai wajen a’adu, da siyasa da mulkin soja kalkashin Louis. Masu ilimin falfasa sun taka rawa mai kyau a lokacin wayewan kai a karni na goma sha takwas (18th), an hambarar da mulukiya a juyin mulkin Faransa. A cikin gadonta da bayanin hakkin ‘dan Adam da na ‘dan Kasa, daya daga cikin takardu na hakkin ‘dan Adam, wanda tana bayyana cewa Kasar ta dace har wa yau. Faransa ta zama daya daga cikin tarihin zamani a jamhuriya na farko sai da Napoliya ya hawo mulki sai ya kafa Daula ta farko na Faransa a shekara alif dari takwas da hudu (1804). Ya dingi fada da rikitattun gwiwa cikin lokacin yake-yaken Napoliya, ya mamaye harkokin Turai fiye da shekaru goma wanda ya shafa al’adun Turai na tsawon lokaci. Faransa ta jimre hayaniyar gadon gwamnatoci a faduwar Daular, mulukiyar ta gyaru. An mayar da shi a shekara ta alif dari takwas da talatin(1830) bisa dokan mulukiya, sannan a gurguje a jamhuriya ta biyu, kuma a Daula ta biyu har zuwa kafuwar jamhuriyar farasanci na uku mai karfi a shekara ta 1870. Jamhuriyar farasanci sun yi rikice-rikice da Ikilisiyar Katolika don rashin wa`azin addinin kirista a faransa a lokacin juyin mulkin farasanci a kafuwar dokar Laicité na shekara 1905. Laicité ya yi tsamani amma haryar cimma buri ne na boko wanda shi ne muhimmin dokan gudanarwa a zamanin yau na hukumar faransanci.

Faransa ta kai tsawo na yankinta cikin karni na sha tara (19) da farkon karni na ashirin (20), zuwa karshe, ta mallaki babban Daula ta biyu na mulkin mallaka a duniya. A yakin Duniya na farko, Faransa ta zo daya daga cikin masu nasara a cikin ninka sau uku tsakanin Kasashe kawance fadan yaki da mulkin tsakiya. Faransa dá kuma daya ne cikiin masu iko a Yakin Duniya na biyu, amma ta zo a kalkashin mamayar kusuwar mulki a shekara ta 1940. Bin kwaton ýanci a shekara ta 1944, Jamhuriya ta hudu ta kafu sai aka narkar da ita a sanadiyar Yakin Aljeriya. An kafa Jamhuriya ta biyar a shekara ta 1958 wanda Charles de Gaulle ya shugabance ta, kuma tana nan har wa yau. Yawancin Daulolin farasanci an bar yin musu mulkin mallaka a Yakin Duniya na biyu.

A cikin tarihinta duka, Faransa ta zama na gaba a duniya da cibiyar al’ada, tana yin muhimmin gudumawa kan Kimiya da Fasaha da Ilimin Falfasa. Faransa ta halarce gaggarumar lamba na uku a kungiyar Kyautata Ilimi da Kimiya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya na Turai a wajajen gadon duniya (bayan Italya da Sfen) kuma tana karban Ýan Yawon Shakatawa kusan miliyan tamanin takwas (83) a shekara fiye da kowane Kasa a duniya. Faransa ta kasance da iko na al’ada muhimi na tattalin arziki, na soja da na siyasa. Ita Kasa ce mai cigaban masana’antu da zama lamba na shida a tattalin arziki a duniya babba ta bin kasafin da Kasa ta tanada, kuma ta zo na tara babba wajen Sayayyan wuta daidaito. Bisa ga Credit Suisse, Faransa ita ce na hudu mafi arziki a Kasashen duniya bisa ga jimilar arzikin gidaje. Ta kuma mallake babban bangare mafi tattalin arziki a duniya (EEZ), wanda Kasarta ta ci murabba’in Kilomita 11,691,000 (4,514,000 sq mi).

‘Yan Farasanci suna jin dadin daidaitacciyar zama, kuma Kasar tana da martaba sosai wajen ilimin Kasashe, kiwon lafiya da ababan rayuwa `yanci da doka ta tanada da kuma raya dan Adam. Faransa tana daga kasashen da sun kafa majalisar Dinkin Duniya wanda ta zama daya daga cikin mambobi biyar na ainihi na ‘yan tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya. Ita kuma mamba ta kungiya ta bakwai (7), Kungiyar Yarjejeniya na Phasa ta Arewa (NATO), Kungiyar Hadin Kai don Rayar da tattalin Arziki (OECD), Kungiyar Sana’a ta Duniya (WTO) da kuma La Francophonie. Faransa ta samar da Tarayyar Turai Kuma na gaba a cikin Tarayyar.

Faransanci

Faransanci (da turanci French) harshen ne da keda asali daga kasar Faransa kuma ya yadu ne a duniya sakamakon shaharar da mutanen Faransa keda shi. Hakane yasa dukkanin kasashen da Faransa ta raina suke amfani da yaren a kasashensu a matsayin yaren kasa.

Fulani

Fulani ko Fulfulde ko Fula wannan duk sunaye ne da ake kiran Fulani dasu, Fulani wasu mutane ne dake a Nijeriya tun a tsawon lokaci, mafi shaharar sana'ar Fulani shine kiyon dabbobin su da saida nono, kuma suna tatsan nonon dabbobin su domin sayarwa, Fulani wasu mutane ne dake kyakkyawan fahimta, ta yadda ya zamanto sukan zauna da kowane kabilu lafiya kuma har su kulla aure a tsakanin su.

Indiya

Indiya tana daga kasashen kudancin Asiya ne, Indiya tanada girma sosai tana kama da gara kuma tanada sahel fadinsa zai kai 700 , Indiya tana da Iyaka da kasashe biyar sune wa'yannan :-

Daga arewa maso yammaci PakistanDaga arewaci Nepal da BhutanArewa maso gabasci Bangladesh da MyanmarDaga kudu maso yammaci 'yan kasashe a tsakiyar ruwaDaga kudu maso gabasci Sri Lanka, da IndonisiyaIndiya itace ta biyu mafi yawan mutane a duniya, Mutanen ta sunkai adadin kusan 1,147,995,900 kuma itace ta bakwai a girman kasa cikin duniya kuma itace cibiyar kasuwanci a tarihince tanada addinai dayawa kamar su ( Hindu, Budha , buza, shitano , sikhiya da Musulunci, tasamu yancin tane daga Birtaniya a shekara ta 1947 .

Kofin kwallon kafar duniya ta 2018

Gasar kofin kwallon kafa ta duniya ta 2018, ko da Turanci 2018 FIFA World Cup shine gasar cin kofin duniya karo na 21 na maza da za'a yi a kasar Rasha da zai gudana a daga ranar 16 ga watan Yuni zuwa 15 ga watan Yuli na shekara 2018.

Wannan shine karon farko da wata kasa daga yankin Turai zata karbi bakuncin gasar tun bayan Gasar kofin duniya ta 2006 data gudana a Jamani. Gasar ce karin farko da zata gudana a yankin gabashin turai kuma karo na 11 a nahiyar Turai. Dukkannin filayen da za'a gudanar da wasannin filayene dake a cikin kasar Rasha.

Gasar ta kunshi kungiyoyin yan wasan kasashe 32. Za'a buga gasar ne filayen wasa 12 a cikin birane 11 na kasar ta Rasha yayin da a ranar 15 ga watan Yuli za'a buga wasan karshe a filin wasa na Luzhniki Stadium dake birnin Mosko na kasar ta Rasha.

Kasar da tayi nasara a gasar itace zata karbi bakuncin gasar FIFA Confederations ta shekarar 2021.

Lagos (birni)

Birnin Lagos, ko Birnin Iko, itace babban birnin Jihar Lagos dake Najeriya, shine birnin da yafi yawan jama'a, sannan kuma birni na biyu da yafi saurin-girma a Afrika, kuma ta bakwai a duniya. Da yawan Lagos birane yankin, bisa ga Lagos gwamnatin jihar ne 17.5 miliyan, da dama jayayya da gwamnatin Nijeriya da kuma hukunci unreliable da National Population Commission of Nigeria. Lagos aka ruwaito a cikin 2014 a yi Metropolitan yawan miliyan 21, yin Lagos mafi girma a Metropolitan yankin a Afrika.

Larabci

Harshen Larabci, itace harshen da mutanen larabawa ke amfani dashi. Da turanci Arabic ko kuma muce larabci a harshen Hausa , Yare ne wanda ya fito daga iyalin yaruruka na AfroAsiya Kuma yare ne wanda ake amfani dashi a yanki gabas ta tsakiya da kuma wasu sassa na kudancin da gabashin nahiyar Afrika dama wasu bangarori na nahiyar Turai .

Yawan mutanen da suke amfani da harshen larabci ya kai Miliyan Dari Biyu Da Chasa'in [290m]

Misra

Kasar Misra ko Masar tana ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta akan marararraba. Ga ta kusa da nahiyar Turai, sannan kuma ga ta a matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar bahar Maliya.

Dalar Giza da ke birnin Al-ƙahirar Kasar. Misra ko kasar Masar dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da 'yar rikitarwa.

Suma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, duk kan waɗannan siffofi, siffofi ne da ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.

Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma 'yan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau kuma wasu dayawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗanda kuma akafi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasalima suna iƙirarin su jinin Afirka ne.

Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta ci gaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya.

Musulunci

Musulunci ko addinin Islama addinin yazo ne daga Annabi Muhammad tsira da amincin Allah sun tabbata agare shi, shine manzon da Allah ya aiko na karshe a duniya domin yasake jaddada addinin Allah na imani da Allah daya wanda Ya halicci kowa da komai. Addinin musulunci nada mabiya a duk fadin Duniya kuma mafiya yawan su na zaune ne a yankin gabas ta tsakiya da yankin Afirka ta arewa wadanda mafiyansu Larabawa ne masu bin adiinin musulunci, sai dai akwai dunbin mabiya addinin musulunci amo INA a fadin Duniyar mu, Ma'anar Addinin Musulunci shine " Yarda da Mika wuya ga kadaituwan Allah Madaukakin Sarki, wato Shaidawa babu abun bautawa da Gaskiya sai Allah kuma Muhammad Manzonsa ne (Ma'aikinsa ne), bayan haka ka yarda da dukkan abubuwan da ya kebanta dasu, da mika wuya ga umarnin Allah Ubangijin talikai, tare da tsarkaka daga kafirci (sanya kishiya wa Allah) da kafirai"Allah Madaukakin Sarki shi ya aiko Manzonsa Annabi Muhammadu (tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da Al Kur'ani Mai Girma domin yazamo shiriya da Rahma ga Halittu baki data, an bayyana musulunci a matsayin addinin dake da saurin karin yawa a duniya a kullum wanda ke da Adadin musulmai na Duniya sun kai kusan kashi 24.1% na dukka mutanen Duniya wato fiye da Musulmai Biliyan Daya da Miliyan dubu dari takwas (1,800,000,000) a fadin duniya.

Nijeriya

Najeriya ko Nijeriya kasa ce dake nahiyar Afirka ta yamma. Tana da al'umman dasu kai fiye da mutum miliyan dari da saba'in da kabilun da suka haura 300. Hasali ma ita ce kasa ta uku a yawan kabilu a duniya. Najeriya ta samu mulkin kanta ne a 1 ga watan oktoba, shekarar 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Najeriya ta yi iyaka da kasashe uku; Daga arewacin kasar, akwai kasar Nijar , daga gabashi akwai Cadi da Kamaru, daga yammacin kasar akwai kasar Benin sannan daga kudancin kasar akwai tekun atalantik ko tabkin Gine.

A da, Lagos ne baban Birnin kasar kuma mazaunin gwamnati, amma a shekarar 1991 aka maida Abuja ta zama babban birnin Najeriya.

Saudi Arebiya

Saudi Arebiya ko Saudiyya wani babban kasa ce dake nahiyar gabas ta tsakiya a Duniya. kasar saudiya ta kasance ne a nahiyar Asiya ko kuma yankin da ake kira da gabas ta tsakiya. Kasar saudiya ta kasance fitacciyar kasa a duniya musamman ta bangaren addini, kasantuwar addinin musulunci yazo ne ta Annabin dayake a wannan yanki, hakama a tattalin arziki Allah ya azurceta ta da dimbin arzikin ma'adinai musamman arzikin man fetur da irin su zinari da gwala-gwalai, ta kasance itace kasar datafi kowacce kasa arzikin man fetur. Lallai kasar saudiya ta kasance kasa ce mai yawan Sahara. kasace mai matukar kyawu sannan Allah ya azurtata da kyawawan bishiyoyi musamman Dabino da Inabi. Kasar saudiya kasace ta Larabawa, Larabci shine yaren kasar.

Tarayyar Amurka

Tarayyar Amurka (da Turanci United States of America) ko Amurka ko Amurika ko Amerika ko Haɗin kan Jahohin Amurika ko Tarayyar Amurka. Jamhuriya ce da ta hada jahohi guda 50 da Yankin fadar kasa da manya manyan kasashe masu cin gashin kai guda biyar. Akwai kuma wasu yankunan marasa yanci guda 11 da ku.a wasu kananan tsibirai guda 9. Amerika na da fadin kasa da yakai sukwaya mil miliyan 3.8 (wato kilo mita 9.8), da kuma adadin mutane miliyan 325, kasar amurika itace kasa ta uku ko ta hudu wajen yawan fadin kasa kuma ta uku wajen yawan mutane. Birnin taraiya shine Washinton Gundumar Kolombiya, birni mafi yawan jama'a da girma kuma shine New York. Jihar Alaska itace a gefen kwanar arewa maso yamma na arewacin Amerika, iyaka da kasar Kanada daga gabas. Rushewar Taraiyar Sibiyat yayi sanadiyyar zaman Amerika kasa mafi karfin iko a duniya kuma Amerika itace kasar da ta gabatar da mulkin demokaradiyya a kasashen duniya da dama.

Mutanen Paleo-Indian ne sukayi hijira daga Rasha zuwa Arewacin Ameruka akalla shekaru 15,000da suka wuce. Mulkin mallakar turawan Birtaniya ya fara ne daga karni na 16. Anyi juyin juya hali na kasar Amerika ya fara ne 1776. An kawo karshen yakinne a shekarar 1783 bayan kafuwar Taraiyar Amurika. Amerika na amfani da Kundin tsarin mulki na 1788, wanda aka sama suna The bill of right. Kasar Amerika itace kasa mafi karfin iko a Duniya tun bayan rushewar Taraiyar. Kuma itace kasar da ta gabatar da mulkin demokaradiyya a wasu daga kasashen duniya.

Kasar Amurika itace ta gabatar da Majalisar Dinkin Duniya, Bankin Duniya, da sauran manyan kungiyoyin duniya.Amerika itace kasa mafi karfin tattalin arzikin duniya da siyasa da kuma al'adu.

Turanci

Turanci harshe ne, kuma yana daga cikin harsunan da ake amfani dasu a nahiyar turai da kasashen dake yammacin duniya, wato nahiyar Amurika ta arewa, shi ne na biyu mafi magana da a harshen a duniya.

Yanar gizo

Intanet ko Yanar gizo wani irin tsari ne na harhade-harhaden na'urorin duniya a bisa bigire guda domin sadar da junansu a bisa dogon zango ba tare da hadakar waya a tsakani ba (wireless). Biliyoyin naurorin computa ne ke jone da juna a babban turken internet a duniya.

Tasirin intanet kan rayuwar Yan'adam

Fasahar intanet fasaha ce da wasu masana ke cewa ta sauya fasalin yadda ake gudanar al'amuran rayuwa a duniya gaba daya, har ta kai wasu na cewa sun fara mantawa da ko yaya rayuwa take kafin zuwan Intanet.

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa

Dan wasan kwallan kafa: Dan wasan kwallon kafa na nufin mutum mai lasisin buga kwallo a fadin duniya ko kuma a farfajiyar yankin da yake bugawa, ko kuma mutumin da yake bugawa domin samun lasisin zama dan kwallo,dan kwallo na da matukar zimma ta yadda ya kasance mai atisayi tukuru domin ganin cewa ya samu rashin gajiyan buga kwallon.Yan kwallo sun karkasu gida da bandaban a cikin fili yayin buga kwallo kamar haka.

Mai tsaran gida(G.K)

Mai kare gida(D.F)

Mai sarrafa tsakiya(M.D.F)

Mai kai hari (C.F)Kowanne dan kwallo a filin kwallo na tsayawa ne tsayin daka domin ganin cewa ya aikata aikin shi domin samar da inganticiyar nasara ga ilahirin tawagar tasu.

Ƙwallo

Ƙwallon ƙafa wasa ne wanda ya samu karbuwa sosai a Duniya; an fara buga ƙwallon ƙafa tun a karni na goma, amma an kafa dokokin wasan a ƙarshen karni na sha tara.

A wasu harsuna

This page is based on a Wikipedia article written by authors (here).
Text is available under the CC BY-SA 3.0 license; additional terms may apply.
Images, videos and audio are available under their respective licenses.